單集摘要
Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani ya duba lamurran siyasar Najeriya da kuma rincabe rikici tsakanin mayakan Houthi na Yamen da Saudia. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani ya duba lamurran siyasar Najeriya da kuma rincabe rikici tsakanin mayakan Houthi na Yamen da Saudia. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
單集
Iran ta nesanta kanta daga rikicin da ke faruwa tsakanin yan Houthi da Saudia
已收聽Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako tare da Oumarou Sani ya duba lamurran siyasar Najeriya da kuma rincabe rikici tsakanin mayakan Houthi na Yamen da Saudia. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
"Mu zagaya Duniya" bitar muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata
已收聽Kamar kowanne mako shirin "Mu zagaya Duniya" ya yi bitar muhimman labaran da suka faru a mako da muke bankwana da shi daga sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa har da rikicin gabas ta tsakiya musamman yadda aka cika shekaru 3 cif da faro yaƙin Isra’ila a Gaza daya kashe fararen hula fiye da dubu 70 wanda kuma shi ya assasa sauran rikice-rikicen da ake gani a yankin, kana a Najeriya da Nijar muka duba halin da ake ciki game da tsadar man fetur sai kuma matsalar tsaro. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya
已收聽A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdinu a matsayin babban abin kunya ga ƙasashen duniya. Masu bincike da suka ɓanƙado yadda jami’an gwamnatin Najeriya na baya da na yanzu suka wawure makuɗan kuɗaɗen talakawa wajen sayen manyan gidaje na ƙasaita a Amurka, sun ce yaƙi da ta’addanci na daga cikin manyan hanyoyi da ake amfani da shi wajen satar dukiyar jama’a a Najeriya. Haka zalika, kotun sasanta rikicin kasuwancin ta duniya dake birnin Paris na Faransa, ta yi watsi da buƙatar Kamfanin Sunrise da ya nemi Najeriya ta biya shi diyyar kuɗi dala miliyan 400.
Ana ci gaba da tsokaci kan mutuwar mutane a hannun Civil Defence na jihar Neja
已收聽Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya tabo batun mutuwar matasa sama da 30 a jihar Neja da ke Najeriya a hannun hukumar tsaro ta Civil Defence. Haka nan Gwamantin Guinea ta aike da gargaɗi a hukumance ga kafofin yaɗa labaran Faransa game da yadda suke kiran sunan shugaban ƙasar, sai kuma Majalisar Ɗinkin Duniya da ta buƙaci masu bincike na ƙasa da ƙasa su karaɗe ilahirin Zirin Gaza, domin tattara hujjoji kan ɗaruruwan gawarwakin mutanen da ake zaƙuluwa daga ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Dangote ya buɗewa al'uma ƙofar shiga a dama dasu a harkokin matatar mai
已收聽Shirin mu zagaya Duniya na wannan ya ba da hankali ne akan yadda Attajirin Afirka Aliko Dangote ya buɗe ƙofar sayar da hannayen jari ga jama'ar Najeriya, sai kuma matakin da mahukuntan Nijar suka ɗauka na umartar masu ababen hawa dasu je Yamai babban birnin ƙasar domin duba lafiyar ababen hawansu, sai batun ladan da Shigaban Amurka Donald Trump ya sanya ladan Dala dubu biyar-biyar ga Amurkawa idan har jam'iyarsa ta Republican ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adi.